Za mu daina sauraren wayoyin jama'a — Obama

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Obama ya ce sauraren wayoyin jama'a ya kare Amurkawa daga hare-hare.

Shugaban Amurka, Barack Obama, ya shaida wa shugabannin kasashen duniya cewa kasarsa za ta daina satar sauraren wayoyin salular da take yi sai dai idan akwai matukar dalilin yin hakan.

A wani jawabi da ya gabatar dangane da sauye-sauye a tsarin satar bayanan wayoyin mutanen da suka hada da 'yan kasar da 'yan kasashen waje, Mista Obama ya yi kira a kawo karshen tattara miliyoyin bayanai na wayoyin tarhon 'yan kasar da gwamnati ke yi.

Shugaba Obama ya ce sanya idanun da suka yi kan hirarrakin da jama'a ke yi ya kare Amurkawa daga fuskantar barazana na tsawon lokaci.

Sai dai ya ce yanzu dole a dauki mataki don ganin ba a yi kutse cikin komai da ya shafi mutane ba.

Kasashen duniya dai sun dawo daga rakiyar Amurka bayan wani tsohon ma'aikacin hukumar leken asirin kasar, Edward Snowden, ya kwarmata bayanan da ke cewa Amurka na sauraren wayoyin jama'a a sassa daban-daban na duniya, ciki har da shugabannin kasashe.

Karin bayani