Harin bom ya hallaka mutane 15 a Kabul

Harin bom a Kabul babban birnin Afganistan Hakkin mallakar hoto
Image caption Harin bom a Kabul babban birnin Afganistan

Mutane 15 sulka mutu a Kabul a wani harin kunar bakin wake da aka kai a wani gidan cin abinci da baki 'yan kasashen waje da jami'an gwamnati ke zuwa.

Wasu 'yan bindiga biyu kuma suka budewa wasu masu cin abinci wuta bayan fashewar bam din.

Babban jam'in 'yan sandan Kabul din Zahir Zahir yace a lokacin da 'yan sanda suka je wajen, 'yan kunar bakin waken sun hallaka.

Cikin wadanda suka mutu a harin dai harda Shugaban asusun bada lamuni a Afganistan Wadil Abdallah.

Kungiyar Taliban dai tace ita ke da alhakin tada wannan bam