Ana Allah-wadai da harin Kabul

Ƙasashen duniya da dama na cigaba da yin Allah-wadai da harin bam na kunar bakin wake da aka kai wani gidan cin abinci na 'yan kasar Lebanon a Kabul, babban birnin Afghanistan.

Harin dai yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla ashirin da daya, kuma yawancinsu 'yan kasashen waje ne.

Ministan harkokin cikin gida na Afghanistan din, Muhammad Umar Daudzai yace, tuni an soma bincike akan lamarin.

Muhammad Umar Daudzai ya kuma ce, an dakatar da jami'an dake kula da mulki da kuma tsaro a unguwar Wazir Akbar Khan inda lamarin ya auku.