An yin tir da harin da aka kai birnin Kabul

Harin da aka kai a Kabul Hakkin mallakar hoto
Image caption Wurinda aka kai harin kunar bakin-wake a Kabul

Kasashen duniya da dama na cigaba da yin Allah-wadai da harin bam na kunar bakin wake da aka kai wani gidan cin abinci na 'yan kasar Lebanon a Kabul, babban birnin Afghanistan.

Harin dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla ashirin da daya, kuma yawancinsu 'yan kasashen waje ne.

Ministan harkokin cikin gida na Afghanistan din, Muhammad Umar Daudzai yace, tuni aka fara bincike a kan lamarin.

Ministan ya kara da cewa, an dakatar da jami'an dake kula da mulki da kuma tsaro a unguwar Wazir Akbar Khan inda lamarin ya auku.

Karin bayani