'Gwamnati ta ƙwace iko da Bor'

Rundunar sojan Sudan ta kudu tace, dakarunta sun kwace iko da garin Bor mai muhimmanci.

Kakakin sojan kasar, Philip Aguer yace, dakarun gwamnati sun yi nasara akan fiye da dakarun 'yan tawaye dubu goma sha biyar dake biyayya ga tsohon mataimakin shugaban, Riek Mashar.

Sai dai kuma garin na Bor, wanda shi ne babban birnin jihar Jonglei ya sha sauya hannu tsakanin 'yan tawaye da gwamnati.

Yanzu dai an shafe kusan wata guda ana fada a kasar Sudan ta kudu.

Fadan dai yana da alaka da kabilanci da kuma siyasa.