Nigeria: 'Akwai buƙatar gyara Al Qibla'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Musulmi suna fuskantar Ka'abah yayin salloli

A Nigeria, samun naurori na zamani yasa wasu a kasar sake yin nazari domin tabbatar da cewar masallatan kasar suna kallon Al-Qibla.

Akasari dai a Nigeria musamman a kasar Hausa, akan danganta Qibla ce da Gabas.

To sai dai wasu na ganin a yayin da gabas din take yin daidai da Al-Qibla a wasu wurare kuwa akwai bukatar karkatawa daga gabas din domin tabbatar da kallon Al-Qiblar.

Ɗaya daga cikin masanan Malam Abubakar Ibrahim ya ce, bincikensu a Kaduna ya nuna masallatai da dama suna buƙatar gyaran Al Qibla.