CAR- Za a yi zaben shugaban rikon kwarya.

Jamhuriyar Tsakiyar Afirka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jamhuriyar Tsakiyar Afirka

Majalisar dokokin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka zata zabi sabon shugaban kasar na rikon kwarya, yayin da ake ci gaba da samun tashin hankali a kasar.

Ko a jiya ma wasu kiristoci sun kashe wasu musulmi biyu, tare da kona gawarwakinsu a wani hari da Kristocin suka ce sun yi domin daukar fansa.

'Yan majalisun sun fitar da sunayen mutane 8 'yan takarar shugabancin kasar na wucin gadi, domin kawo karshen tashin hankalin da kasar ke ciki na tsawon watanni.

Cikin wadanda aka fitar da sunayen nasu har da 'yayan biyu daga cikin tsoffin shugabanni Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar.

'Yan majalisar za su zabi mutum guda cikin takwas din da zai jagoranci kasar na wucin gadi, bayan da shugaban kasar Michel Djitodia yayi murabus saboda matsain lambar kasashen duniya, kan gazawarsa wajen kawo karshen zub da jinin da ake yi a kasar.