An soke zaben kananan hukumomi 2 a Jigawa

Zaben kananan hukumomi a jihar Jigawar Najeriya Hakkin mallakar hoto b
Image caption Zaben kananan hukumomi a jihar Jigawar Najeriya

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Jigawa ta soke zaben kananan hukumomin biyu, a zaben da aka yi ranar Asabar din da ta gabata.

Kananan hukumomin sune na Hadejia da kuma Malam Madori.

Wata takarda da kakakin hukumar zaben ya sanyawa hannu, ta ambato cewa an soke zaben ne sakamakon satar akwatuna da tashe- tashe hankula, wanda hukumar tace ya shafi ingancin zaben da nagartar sa.

Magoya bayan jam'iyyar APC dai sun yi zaman dirshen tun yammacin ranar Asabar har zuwa daren Lahadi, inda suke jira a bayyana sakamakon zaben, Wanda aka ce an nemi jami'an da zasu bayyana sakamakon sama ko kasa an rasa.

Jam'iyar APC a jihar ta ce tana Allah wadai da yadda hukumar zaben ta gudanar da zaben kananan hukumomin.