An tara kudaden taimaka ma garin Arlit, a Nijar

Wurin aikin hakar Uranium a Arlit
Image caption Wurin aikin hakar uranium a Arlit

A jamhuriyar Nijar, hukumomi tare da kungiyoyin farar hula na Arlit sun fito da wani shiri domin kyautata jin dadin rayuwar al'umomin karamar hukumar.

Tsabar kudi sama da biliyan 3 ne na cfa karamar hukumar ke bukata domin tafiyar da ayyuka iri iri da suka hada da gina hanyoyin zirga zirga, da samar da wutar lantarki a cikin garin Arlit.

Hukumomin karamar hukumar dai sun shirya wani taro ne a Yamai domin jawo hankalin abokan arziki masu hannu da shuni, kuma tuni aka bude wata gidauniya domin tattara kudaden tafiyar da ayyukan.

A lokacin taron sun tara sama da miliyan dari uku na CFA.