Najeriya- Jam'iyar PDP za ta sanar da sabon shugaba

Helkwatar Jam'iyar PDP mai mulkin Najeriya
Image caption Helkwatar Jam'iyar PDP mai mulkin Najeriya

Majalisar koli ta zartarwar jam'iyyar PDP a Najeriya zata sanar da wanda zai maye gurbin tsohon shugaban jam'iyyar Alhaji Bamanga Tukur.

Alhaji Bamanga Tukur yayi murabus ne bayan matsin-lambar da ya fuskanta daga wasu manyan 'ya'yan jam'iyyar, wadanda ke zargin cewa ya zama dan amshin-shatan bangaren zartarwa.

Jam'iyyar ta PDP dai ta kebe wannan kujerar ne ga shiyyar arewa-maso-gabashin Najeriyar.

Rahotanni sun yi ta ambato mutane da dama dake zawarcin wannan mukami na shugaban jam'iyar PDP na kasa wadanda suka fito daga shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar.

An dai dauki tsawon lokaci ana sa-in-sa da wasu 'yayan jam'iyar PDP musamman ma gwamnoni, kafin tsohon shugaban Bamanga Tukur ya yi murabus daga mukaminsa a makon jiya.

Hakan dai ya kai ga darewar jam'iyar gida biyu bayan ballewar wasu da suka kira kansu da 'yan sabuwar PDP, inda daga bisani suka koma babbar jam'iyar adawa ta APC.