Ukraine: 'Yan adawa sun yi gangami

Hakkin mallakar hoto Reuters

Dubban masu adawa da gwamnati ne suka hallara domin yin gangami a Kiev, babban birnin Ukraine, duk da sabuwar dokar da ta takaita yin zanga-zanga a kasar.

Yawancin masu zanga-zangar sun rufe fuskokinsu, domin bijirewa sabuwar dokar wacce ta haramta rufe fuskoki yayin zanga-zanga.

Dokar wacce shugaba Victor Yanukovich ya sanyawa hannu ranar Juma'a ta kara harzuka 'yan adawa wadanda a cikin kwanakin baya fafutukarsu ta dan lafa.

An dai soma zanga-zanga a kasar ne tun daga lokacin da Ukraine ta fice daga tattaunawar karfafa huldar tattalin arziki da kasashen kungiyar tarayyar turai.