Ukraine- Shugaba Yanukovych zai kaddamar da wata hukuma

Zanga-zanga a kasar Ukraine Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zanga-zanga a kasar Ukraine

Shugaban kasar Ukraine Viktor Yanukovych zai kaddamar da hukuma ta musamman don nemo warware rikicin siyasar da aka shafe makonni ana yi.

Sanarwar ta fito ne bayan yini guda da aka shafe ana fito-na-fito tsakanin 'yansandan kwantar da tarzoma da masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a birin Kiev, inda aka bankawa ababan hawa wuta tare da jefe-jefe.

Daruruwan mutane ne dai suka jikkata a arangamar.

'Yan sandan kwantar da tarzomar sun yi arangama da dubban masu adawa da gwamnati dake yin Allah-wadai da sabuwar dokar da ta takaita yin zanga-zanga a kasar.

Yawancin masu zanga-zangar sun rufe fuskokinsu, domin bijirewa sabuwar dokar wacce ta haramta rufe fuskoki yayin zanga-zanga

Amurka ta yi kiran da gaggauta kawo karshen tashe-tashen hankulan da aka fara watanni biyun da suka gabata, bayan da shugaban kasar ya janye daga tattaunawar karfafa huldar tattalin arziki da kasashen Kungiyar Tarayyar Turai, ya kuma maida hankali kan karfafa alaka da kasar Rasha.