Boko Haram sun kashe mutane 15

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mazauna yankin sun ce mutane da daga sun tsallaka zuwa Nijar

Wasu da ake zargi 'yan Boko Haram ne sun kashe mutane 15 a jihar Borno da ke Nigeria.

Mutanen kauyukan da ke kan iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar da kuma 'yan sanda sun ce daruruwan mutane sun gudu daga yankin inda suka tsallaka Nijar bayan kai hare-haren.

Mutanen yankin sun shaidawa BBC cewa mutum bakwai aka kashe, alkaluman da kwamishinan 'yan sandan jihar Borno, Gideon Jibrin, ya tabbatar.

Sai dai ya kara da cewa an nutsar da mutane uku a cikin wani ruwa lokacin da suke gujewa hare-haren a kauyen Gashigar.

Karin bayani