CAR: Samba-Panza ce sabuwar shugabar kasa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Catherine Samba-Panza, sabuwar shugabar kasar

Majalisar dokokin jamhuriyar Afrika ta tsakiya ta zabi Catherine Samba-Panza a matsayin shugabar riko.

Ms Samba-Panza wacce itace magajin garin birnin Bangui, na da alhakin maidoda zaman lafiya a kasar dake fama da rikicin addinni.

Ta maye gurbin Michel Djotodia shugaban 'yan tawayen Seleka wanda ya kwace mulki a watan Maris.

Djotodia ya sauka ne bayan matsayin lamba daga kasashen waje, bayan ya kasa kawo karshen zubar jini.

Ministocin harkokin wajen kasashen tarayyar Turai sun amince su tura karin dakaru don hadewa da sojojin Faransa da na Afrika wadanda ke ayyukan kawo zaman lafiya a kasar.

Karin bayani