An kashe mutane akalla 18 a jahar Borno

Hari a jahar Borno Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hari a jahar Borno

Rahotanni daga jahar Borno da ke arewacin Najeriya sun ce an kai hari a kauyen Alau Ngawo inda aka hallaka mutane 18.

An kuma ce an kona gidaje da dama a harin da aka kai a daren Lahadi zuwa Litinin.

Da dama daga cikin mazauna garin da suka tsira da rayukansu sun kaura zuwa wasu wurare na dabam saboda fargabar a kai masu wani sabon harin.

Kanar Muhammed Dole, kakakin rundunar sojojin Najeriya ta 7 da ke Maiduguri ya tabbatar da kai harin.

To amma ya ce ba su da cikakkun bayyanai game da harin.

A cikin wata hira da kafofin watsa labarai, mai garin kauyen na Alau Ngawo ya ce mutane 18 ne suka mutu.

Wannan yanki na Najeriyar na fama da kashe kashen da ake dangantawa da kungiyar Boko Haram.

Sabon shugaban sojojin kasar, Alex Badeh, ya yi kiran da a kawo karshen tada kayar bayan ba tare da bata lokaci ba.