Aikin dare na haddasa cututtuka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Aikin dare a hanyar jirgin kasa na London

Aikin dare na hargitsa jiki tare da haddasa cututtuka masu dogon zango, a cewar masana kimiyya.

A baya dai an tabbatar da cewa masu yin aiki da daddare sun fi shiga hatsarin kamuwa da cutar sukari, ciwon zuciya da kuma kansa, wato daji.

A yanzu kuma masana a cibiyar bincike game da barci a garin Surrey dake Ingila sun gano cewa aikin dare na tasiri kan kwayoyin halittar bil'adama.

Kwararrun sun ce sun yi matukar mamakin girma, sauri, da tsananin irin barnar da kasancewa a farke da daddare ke yi wa halittar bil'adama.

Halittar jikin mutum dai ta ginu ne kan barci da daddare da kuzari da rana.

Don haka aikin dare na da mummunan tasiri ga jikin mutum, inda yake sauya gudanar ruwan jiki, dumin jiki, kuzari, da kuma aikin kwakwalwa.

Jiki kan rikirkice

Binciken ya yi nazari ne kan mutane 22 da aka sauya musu aiki daga rana zuwa dare.

Gwajin jinin da aka yi musu ya nuna cewa kimanin kaso 6% na kwayoyin halittar jikin mutum na gudanar da ayyukansu ne a wasu kebantattun lokuta na yini.

Don haka da zarar mutum ya fara aikin dare sai wannan tsarin ya wargaje.

"Fiye da kaso 97% na kwayoyin halittar kan sauya yanayin aikinsu idan ba'a yi barci a lokacinsa ba, abinda ke sa mu rashin jin dadi idan mun yi doguwar tafiya a jirgin sama, ko kuma idan mu na aikin dare," a cewar Dr Simon Archer, daya daga cikin masu binciken a jami'ar Surrey.

Abokin bincikensa Farfesa Derk-Jan Dijk ya ce duk wata gabar jikin mutum na da tsarin aikinta kuma aikin dare na wargaza tsarin ta yadda zuciya za ta saba wa koda ita kuma ta saba wa kwakwalwa.

Ya shaida wa BBC cewa: "Jiki kan rikirkice. Kamar rayuwa ne a cikin gidan da kowanne daki yake da agogo kuma kowanne agogon na bada lokaci dabam, wanda zai haifar da rudani a cikin gidan."

Tasirinsa babu tabbas

Binciken ya nuna cewa masu aikin dare wanda ke samun barci kadan a lokacin da ba na barcin ba sun fi shiga hadarin kamuwa da ciwon sukari da kuma tara taiba.

Haka kuma ciwon zuciya yafi yaduwa tsakanin masu aikin dare.

Farfesa Hugh Piggins na jami'ar Manchester ya shaida wa BBC cewa binciken ya fitar da tsananin illar da aikin dare ke iya yi wa dan Adam.

Sai dai ya ce gajeren bincike ne don haka babu tabbas akan tasirinsa.