An dawo da tattaunawa kan Syria

Shugaba Basharul Assad na Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ko da yaushe dai gwamnatin Syria na musanta zargin musgunawa 'yan kasar.

An dawo da shirye-shiryen tattaunawar Sulhu kan rikicin Syria, bayan da Sakatare Janal na Majalisar Dinkin Duniya ya janye goron gayyatar da ya ba kasar Iran a tattaunawar.

Matakin da Mr Ban ki-Moon ya dauka ya kawo karshen abin da wakilin BBC ya kira da sa'o'i ashirin da hudu na rudanin diplomasiyya, wanda ya taso sakamakon gayyatar da Sakatre Janal din ya yi wa Iran dan ta shiga tattunawar da ake akan Syria.

Mai magana da yawun sakataren ya ce, "Ban ki-Moon ya nuna rashin jin dadinsa da rashin fitowar Iran karara da nuna goyan bayanta ga kafa gwamnatin rikon kwarya a Syria."

A yanzu dai babbar kungiyar adawa ta Syria da ita kan ta kasar Amurka sun janye barazanar da suka yi na kauracewa taron.

Sai dai tun da fari Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce kuskure ne ace babu Iran a tattaunawar, ya kuma ce daman haka tattaunawar sulhu ta gada, ba lallai bane ta hada mutanen da kake so, abu mai muhimmanci shi ne shigo da mutanen da za su kawo maslaha.

Karin bayani