CAR: Kalubalen dake gaban Samba-Panza

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kalubalen sulhu tsakanin musulmai da kirista ne a gaban sabuwar Shugabar CAR

A Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya an zabi magajiyar garin Bangui Catherine Samba-Panza a matsayin shugabar kasar ta wucin gadi.

Mrs Samba-Panza gogaggiyar lauya ce da ta samu horo a kasar Faransa, babban kalubale na farko da za ta fuskanta shi ne na kawo karshen rikicin da kasar ke ciki.

Tun da fari ta yi kira ga Musulmi da Kirista da ke fada da junansu da su ajiye makamansu.

Babbar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya Navi Pillay ta bukaci kasashen duniya da su dauki mataki dan kawo karshen zubar da jinin da ake yi a Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya.

Ministocin Tarayyar Turai suma sun amince da a kara tura wasu dubban dakarun soji kasar, domin su hade da dakarun sojin Faransa da na kasashen Afrika dan wanzar da zaman lafiya.

Karin bayani