Kararrakin fyade na karuwa a Kano

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mata a jihar Kano na fuskantar barazanar fyade.

Gwamnatin jihar Kano dake arewacin Nigeria ta ce an samu karuwar kararrakin fyade ga mata a jihar.

Kwamishinan shari'a na jihar, Barista Maliki Kuliya Umar ya ce a cikin watannin Nuwamba da Disamban bara an shigar da kararrakin fyade 100 a kotunan jihar.

Barista Umar ya ce an yanke wa mutane 40 daga cikin wadanda ake zargin hukuncin dauri a gidan yari.

Ya kuma ce akwai kuma dimbin zarge-zargen fyaden da aka sasanta ba tare da zuwa kotu ba.

A cewar kwamishinan, adadin kararrakin ya karu ne bayan da iyaye da 'yan uwan wadanda aka yi wa fyaden suka fahimci muhimmancin neman hakkinsu, maimakon boye-boye da akan yi a da saboda gudun tsangwama.

Karin bayani