Komla Dumor: Fuska da muryar Afrika

Image caption Margayi Komla Dumor

Sakamakon rasuwar mai gabatar da shirye-shirye na BBC, Komla Dumor mai shekaru 41, Editan Afrika na BBC Solomon Mugera ya yi waiwaye a kan irin kyawawan ayyukan marigayin.

Komla Dumor ya kasance fuska kuma muryar Afrika -matashi mai kwazo da sadaukar da kai da kuma dabi'u na gari.

Lokacin da ya soma gabatar da shirin kasuwanci na Afrika na BBC, ya fito da kalubalen da nahiyar ke fuskanta da kuma irin ci gaban da ake samu a nahiyar sakamakon bunkasar tattalin arziki.

Image caption Margayi Komla tare da tsohon ma'aikacin BBC Muhammed Jameel Yusha'u a shekara ta 2010

Ya ziyarci kasashen Afrika da dama kuma ya kasance mai duba duka bangarorin labari don yin adalci.

'Aikin Rediyo'

An haifeshi a Ghana, kuma iyayensa malaman makaranta ne.

An bukaci Komla ya zama likita amma sai ya zama dan jarida.

Ya shiga jam'iyyar Jos a Nigeria a karshen shekarun 1980 don ya karanci aikin likita.

Dan uwansa Korshie, shi ya tsaya ya zama likita shi kuma Komla da ya bar karatunsa a Nigeria sai ya koma Ghana inda ya karanci nazarin zamantakewa da halayyar dan Adam.

Image caption Margayi Komla tare da Aliyu Abdullahi Tanko lokacin gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu a shekara ta 2010

A lokacin da ake yajin aiki a Jami'ar Ghana a shekarar 1998, sai ya samu aiki a matsayin mai dauko rahotanni a kan zirga-zirgar ababen hawa a kan tituna aa gidan rediyon Joy FM.

Daga nan ne kuma ya soma aiki a matsayin ma'aikacin rediyo.

Sai kuma a shekara ta 2000 gidan rediyon Joy FM ta bashi wani shiri da ake gabatar wa da safe, abinda ya sa shi farin jini a daukacin Ghana.

'Dan Baiwa'

Mahaifiyarsa Cecelia Dumor na da babban digiri a fannin koyan aikin jarida.

Mutane na ganin cewar watakila ita ce ta koya wa Komla aikin jarida kafin rasuwarta a shekarar 2008.

Mahaifinsa, Ernest Dumor Farfesa ne a fannin nazarin zamantakewar al'umma.

Image caption Margayi Komla tare da Haruna Shehu Tangaza a harabar ofishin BBC a London a 2013.

Kakansa Philip Gbeho sanannen mawaki ne kuma tsohon shugaban Ghana, Kwame Nkrumah ya bukace shi ya tsara taken kasar a shekarar 1957 lokacin da suka samu 'yancin kai.

Komla ya na da shaidar karatun babban digiri a jam'iar Harvard, sannan ya auri matarsa Lauya Kwansema a shekara ta 2001.

Ya rasu ya bar 'ya'ya uku: Elinam Makafui 'yar shekaru 11 da Elorm Afadzinam dan shekaru 8 da kuma 'yarsa Emefa Araba 'yar shekaru biyu.

Za a dinga tunawa da Komla Dumor saboda saukin kansa da barkwanci da kuma haba-haba da jama'a.