'Yan majalisu za su dawo aiki a Nigeria

Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption 'Yan majlisun Najeriya ka iya tattaunawa kan shugabancin Majalisar

A Najeriya, ranar Talata ne 'yan majalisun dokokin kasar za su koma bakin aiki, bayan wani hutu da suka yi na bikin Kirsimeti da shigar sabuwar shekara.

'Yan majalisar dai sun tafi hutu bayan ministar kudin kasar, Ngozi Okonjo-Iweala ta gabatar musu da kudirin kasafin kudin kasar na bana.

Kazalika a daidai lokacin ne ake maganar sauye-sauye a jagorancin majalisar wakilan kasar sakamakon sauya sheka da wasu 'yan majalisar su 37 suka yi daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Masu nazarin al'amura za su sa ido a zaman na Talata su ga abinda zai wakana a majalisar.

Karin bayani