Nijar ta kaddamar da shirin kayyade iyali

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Matan Nijar sun fi na ko'ina yawan haihuwa.

Hukumomin kiwon lafiya a Nijar tare da hadin gwiwar hukumar ayyukan cigaba a kasashen a waje ta Amurka wato USAID, sun kaddamar da wani shirin kayyade iyali.

A karkashin shirin, mata za su rika amfani ne da magungunan hana daukar ciki domin bada tazara a tsakanin haihuwa.

Hukumomin sun ce hakan zai taimaka wurin inganta lafiyar matan da jariran da suke haifa.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce matan Nijar sun fi na kowacce kasa yawan haihuwa inda kowacce mace kan haifi 'ya'ya bakwai zuwa takwas.

Karin bayani