Rasha ta soki cire Iran daga taron Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sergei Lavrov ya ce cire Iran kuskure ne

Rasha ta soki Majalisar Dinkin Duniya bisa cire Iran daga cikin kasashen da zasu yi tattaunawar sulhunta rikicin Syria ranar Laraba.

Ministan hulda da kasashen wajen Rasha, Sergei Lavrov ya ce halartar Iran na da muhimmanci ga nasarar tattaunawar da aka yi wa lakabi da Geneva Two.

Iran tayi tur da hanata shiga taron.

Sakatare janar na majalisar, Ban Ki-Moon yace Iran taki ta bayyana goyon bayanta ga kafa gwamnatin rikon kwarya a Syria, abinda shi ne tushen tattaunawar.