An gano shaidu kan azabtarwa a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An sami hotunan gawawaki da alamun dukan kawo wuka a Syria

Wani rahoto da wasu tsofaffin masu shigar da kara a kotun hukunta laifukan yaki su uku suka gabatar ya ce Syria ta musguna tare da kashe kimanin mutane 11,000 da ake tsare da su tun lokacin da aka fara boren kin gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad.

Masu binciken sun duba hotunan matattun fursunonin da aka yi fasa kwaurinsu daga Syria da wani soja ya dauka; hotunan sun nun wasu fursunonin an yi musu dukan kawo wuka wasu kuma gawar ta su ba kyaun gani.

Daya daga cikin wandanda suka gudanar da binciken Farfesa Sir Geoffey Nice ya shaidawa BBC cewa wadannan manyan hujjoji ne da suka bayyana hannun gwamnatin Syria kan kisan mutanen.

A lokuta mabanbanta kuma kan batutuwa daban-daban BBC ta yi kokarin tuntubar gwamnatin Syria amma hakan ya ci tura.

Karin bayani