Sammacin kama babban jami'in Vatican

Bankin Vatican Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bankin Vatican

An bayar da sammacin kama wani babban jami'in cocin fadar Paparoma ta Vatican, kuma akanta, kan zargin halatta kudaden haram da kuma aikata zamba.

Masu gabatar da kara sun zargi Monsignor Nunzio Scarano da wawure kudaden gudunmawar sadaka da aka baiwa wani gidan masu ciwon mutu ka raba a kudancin Italiya.

An ce yayi amfani da kudaden wajen biyan bashin da ya karba don sayen gidansa.

Da ma Monsignor Scarano na cikin daurin talala, kuma ana masa shari'a a kan zargin yunkurin fasa kwaurin dala miliyan 20 daga Switzerland.

Fadar Paparoma ta Vatican ta sha nema wa jami'anta kariyar diplomasiya.

To amma Paparoma Francis yayi alkawarin kawar da cin hanci da kuma tabbatar da cewar ba a yi amfani da bankin fadar ta Vatican ba wajen halatta kudaden haram.