Tagwayen shadda sun ja cece-kuce a Rasha

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tagwayen shadda a Sochi, Rasha

Wani hoto da BBC ta wallafa na wurin bahaya mai matsugunnai biyu a daya daga cikin wuraren da za a gudanar da wasannin Olympics na lokacin sanyi a garin Sochi dake Rasha ya jawo cece-kuce a twitter.

Mutane da yawa, ciki har da jagoran 'yan adawa Alexei Navalny ne suka yi sharhi kan hoton da wakilin BBC a Moscow Steve Rosenberg ya dauka a cibiyar 'yan jaridu ta gasar Olympics na Sochi.

Mr Navalny ya yi mamakin yadda aka kashe $50biliyan (Naira tiriliyan 8.5) din da aka ce an ware wa wasannin idan har aka kasa samar da kadaici a bandaki.

Wadansu kuma hoton mamaki ya basu ko kuma dariya, yayin da wasu masu sharhin ke alakanta shi da magangunan da ake yi a baya bayan nan game da hakkin 'yan luwadi da madigo a Rasha.

Mr Navalny ya sake yada hoton tare da sharhin: "Wannan bandakin maza ne a cibiyar 'yan jaridu ta gasar Olympics na Sochi wacce aka gina kan rouble biliyan 1.5 (Naira biliyan 76.5).

Hakkin luwadi da madigo

Image caption Gandun matsuganai a jami'ar Kazan, Rasha.

Wadansu kuma sun yi amfani da damar wurin muzanta dokar hana yada luwadi da madigo da Rasha ta zartar, wacce ta sa masu fafutuka kira ga kasashen duniya su kaurace wa wasannin da za a yi a Fabrairu.

Wani daga cikinsu cewa yayi, "da alama haka suka fahimci kare hakkin masu luwadi da madigo".

Kusan shekaru biyu da suka wuce aka kammala ginin cibiyar, tare da gudunmawar kamfanin man fetur na gwamnatin Rasha, Gazprom.

A lokacin da aka kammala shi wani kakakin kamfanin ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Rasha, Interfax cewa; "Ginin na daya daga cikin mafi girma da wadatar kayan more rayuwa irinsa a fadin duniya."

Koda yake ba safai akan samu tagwayen matsugai a bandaki daya a sassan Rasha dake nahiyar Turai ba, dan jaridar Rasha Nikita Likhachev ya ce wannan ba bakon abu ba ne a wasu sassan kasar.

Misalan da ya bayar kuwa sun hada da wasu wuraren wasannin da kuma gidajen cin abinci.