Za mu yi zaben 2015 bisa adalci - Jega

Hakkin mallakar hoto b
Image caption Jama'a sun yi korafi kan yadda aka yi zaben 2011

Hukumar zabe a Nigeria, INEC ta ce ta soma shiri kan yadda za ta gudanar da zabukan kasar na shekarar 2015, cikin gaskiya da adalci.

Shugaban hukumar, Farfesa Attahiru Jega ne ya bayyana haka a hirarsa da manema labarai a Kaduna, lokacin taron da hukumar ta shirya wa manyan jami'anta don waiwayen yadda aka gudanar da zaben 2011 da kuma yadda za a gujewa kura-kurai a zabukan dake tafe.

Farfesa Jega ya ce su na shiri don ganin an gudanar da zabukan 2015 ba tare da 'magudi' ba, kuma cikin gaskiya bisa tsarin dokar kasar.

A cewarsa, aikin zabe ba a rasa suka da korafe-korafe daga wajen jama'a amma dai za su ci gaba da aiki don tabbatar da inganci a zabukan da ke tafe.

Karin bayani