An kama 'yan Mafia 90 a Italy

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Zanga-zangar adawa da Mafia na karuwa a Italy

'Yan sandan Italy sun kama akalla mutane 90 bisa zargin su na da alaka da 'yan Mafia.

An kuma kwace kadarori a hare-haren da aka kai a garuruwan Rome, Naples da Florence.

Kamen dai yafi mai da hankali ne kan iyalin Contini dake cikin kungiyar Mafia ta Camorra dake da tushe a Naples.

'Yan sanda sun kuma binciki gidajen giya da kantunan sayar da abinci da iyalin ya mallaka.

Wakilin BBC ya ce kamen na kara bayyana damuwar cewa 'yan Mafia na kudancin Italy na kara kutsawa arewacin kasar.