Dattawan Arewa za su kai Ihejirika ICC

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kona gidaje da motoci a tashin hankali a garin Bama

Kungiyar dattawan arewacin Najeriya ta ce za ta gurfanar da tsohon babban hafsan sojin kasar Laftanar Janar Azubuike Ihejirika a gaban kotun hukunta laifuffukan yaki ta duniya watau ICC.

Shugabannin kungiyar sun zarge tsohon babban hafsan sojin kasar da baiwa sojoji umurnin kashe mutane a garin Bama na jihar Borno.

Mai magana da yawun kungiyar, Farfesa Ango Abdullahi ya bayyanawa manema labarai cewar binciken da suka gudanar sun nuna cewar tsohon babban jami'in sojan Kasar, ya bada umurnin kashe fararen hula a jihar ta Borno abinda ya nuna cewar an keta hakkin bil adama.

Jihar Borno na daga cikin jihohin da ake fama da tashin hankali mai nasaba da kungiyar Boko Haram.

Dubban mutane ne suka mutu sakamakon rikicin 'yan Boko Haram ciki hadda jami'an tsaro da kuma fararen hula.

Karin bayani