An nemi cire Speton 'yan sandan Najeriya

Hakkin mallakar hoto Aliyu
Image caption Ana zargin M D Abubakar da kasa aikinsa

A Najeriya, wasu 'yan majalisar dokoki sun bukaci a sauke Babban Sipeta-janar na 'yan sandan kasar, Muhammad Dahiru Abubakar, bisa zarginsa da gaza kawo karshen rikicin da ake fama da shi a jihar Rivers da ke kudu-maso-kudancin kasar.

'Yan majalisar dai sun yi zargin cewa da hannun 'yan sanda a harin da aka kai wani taro a jihar.

An yi zargin dai an harbi wani Sanata, tare da halaka wasu yara biyar.

Wannan batu ya kara zafafa siyasar Jihar ta Rivers da kuma zarge-zargen hannu dumu dumu na Jami'an tsaro kan rikicin.

Karin bayani