Za a fara tattaunawar Sulhu kan Syria

Image caption Syria za ta hadu da 'yan adawa

A ranar Laraba ne za a fara tattaunawa kan batun rikicin Syria da aka dade ana jiran lokacin a birnin Montreux na Switzerland.

Wannan ita ce tattunawar gaba da gaba ta farko tsakanin bangarori biyu masu adawa da juna tun fara yakin na Syria shekaru uku da suka gabata.

Sai da aka yi matsin lambar diplomasiyya kafin a samu wasu daga cikin 'yan adawa su shiga tattaunawar yayin da wasu suka bijire.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ne zai jagoranci taron.

Za a fara tattaunawa don cimma yarjejeniya kan batutuwan da suka hada da tsagaita wuta da kuma ba da dama ga kungiyoyin agaji don isa ga jama'ar da suka galabaita.

Karin bayani