Cacar baki a taron sulhu kan Syria

Image caption Wakilin gwamnati da kuma na 'yan adawar Syria

An soma tattaunawar neman wanzar da zaman lafiya ta kasashen duniya domin kawo karshen yakin basasar kasar Syria a wani wurin shakatawa na Montreux a Switzerland.

Karuwar tada jijiyoyin wuya tsakanin wakilan gwamnatin Syria da babbar kungiyar 'yan adawa ta bayyana a jawaban bude taron da dukanin bangarorin su ka yi.

Shugaban 'yan adawa Ahmed Jarba ya zargi Shugaba Bashar Al-Assad da aikata laifukan yaki sannan ya hakikance cewar bai kamata ya kasance da wani hannu a makomar siyasar Syria ba.

Ministan harkokin wajen Syria Walid Muallem ya bayyana 'yan adawar a matsayin maciya amanar kasa sannan kuma 'yan barandan kasashen waje.

Sannan a cewarsa Shugaba Assad ba zai mika wuya ga bukatun kasashen waje na ya sauka ba.

Karin bayani