APC na horar da 'yan bindiga - PDP

Hakkin mallakar hoto no
Image caption Gwamnan Imo Rochas Okorocha ya musanta zargin ya na horar da 'yan bindigar APC saboda zaben 2015

Jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria ta zargi jam'iyyar adawa ta APC da horar da wasu matasa a jihar Imo da ke kudancin kasar yadda ake sarrafa makamai.

Jam'iyyar ta ce matasan da aka tattaro daga jihohi daban-dabam na Nigeria, ciki har da jihohin arewacin kasar, za a iya amfani da su domin kai farmaki ga abokan adawa lokacin zabubbukan gama-gari na 2015.

Sai dai gwamnatin jihar Imo ta yi watsi da wannan zargin da ta kira soki-burutsu ne kawai irin na 'yan adawa.

Ta kuma kalubalanci jam'iyyar PDP da ta gaiyaci 'yan sanda su gudanar da bincike.

Kawo yanzu dai hukumar 'yan sandan jihar ta ce ba ta da wata masaniya game da zargin.

Karin bayani