Jagoran Chechnya na kokawa da ministoci

Ramzan Kadyrov, shugaban yankin Chechnya na kasar Rasha, ya yi maraba da zubar dusar kankara ta farko a birnin Grozny a bana, ta hanyar kokawa da ministocinsa.

Tsohon dan tada kayar bayan da ya zamo shugaban Chechnya kusan shekaru bakwai da suka wuce ne ya wallafi hotunan kokawar a shafinsa na Instagram.

Ya kuma rubuta cewa: "Salaam aleikum abokaina!. Bayan fitowa daga tattaunawar da na ga ba ta yi wa wasu daga cikinmu dadi ba, na dauki matakin farantawa ministocina...Gaisuwa gare ku ranar zubar dusar kankara ta farko!

Fiye da mutane 9,300 ne suka danna alamar son hoton, yayin da fiye da sharhi 20 cikin harsunan Larabci, Rashanci, da Chechen ne suka yaba wa Mr Kadyrov.

"Ya na tuna kuruciyarsa, ya na salla akan kari kuma yafi duk shugabannin yankin nan haduwa", a cewar daya daga cikin masu sharhin.

Kishin Islama

An dai ta goge batutuwan wadanda suka soki shugaban kasar - amma dai mafi yawansu na zargin Mr Kadyrov ne da handame kudaden tallafin da yake samu daga Rasha.

Mr Kadyrov ya wallafa hotunan ne kwanaki kadan bayan da ya rubuta wani bayani a Instagram cewa an kashe wani dan bindigar Chechnya da ya bukaci mabiyansa su kai hari kan wasannin Olympics na hunturu da za a gudanar a Sochi.

Dakarun Rasha dai na kai farmaki kan 'yan bindiga masu kishin Islama daga Chechnya da kuma jamhuriyoyin Dagestan da Ingushetia masu makwabtaka, a shirye-shiryen fara wasannin Olympics ranar 7 ga Fabrairu.