Za a kara saurin sakonnin intanet

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An aika sakon daga hasumiyar BT zuwa Ipswich

An yi nasarar aika sakon intanet mafi sauri a duniya a wani gwaji da aka yi a London, abin da ke karfafa zaton za a yi inganta tura sako ba tare da sauya na'urorin da ake amfani da su ba.

Kamfanonin sadarwa na Alcatel-Lucent da BT sun ce sun tura sako da ya yi saura terabits 1.4 cikin sakan daya - daidai da aike wa da finafinai 44 cikin sakan daya.

An aika sakon ne nisan kilomita 410 tsakanin hasumiyar BT da ke tsakiyar London zuwa garin Ipswich.

Sai dai za a iya shekaru kafin masu amfani da na'urorin sadarwa su ga wani bambanci.

Duk da haka ana daukar sakamakon a matsayin gagarumar nasara ga kamfanonin samar da fasahar intanet domin zai ba da damar tura sakonni masu dimbin yawa ba tare da kashe kudi wurin kara karfi da girman na'urorinsu ba.

Kamfanin Alcatel-Lucent ya shaida wa BBC cewa kowa ce shekara akan samu bukatar karin saurin intanet da kaso 35% musamman saboda karuwar masu kallon finafinai ta intanet.