Morocco ta soke "auren fyade"

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Majalisar dokokin Morocco

Majalisar dokokin Morocco ta soke dokar da ta bada dama ga mazajen da suka yi wa 'yan mata fyade su gujewa tuhuma ta hanyar aurensu.

An kada kuri'ar ne shekaru biyu bayan da wata yarinya 'yar shekaru 16, Amina al-Falali ta kashe kanta, saboda iyayenta da mai shari'a sun amince da aura ma ta wanda ya yi ma ta fyade domin kare martabar iyayen nata.

Lamarin dai ya girgiza al'umar Morocco, har ya janyo gagarumar zanga-zanga a Rabat, babban birnin kasar da sauran biranen Morocco.

Masu rajin kare hakkin mata a kasar sun yi marhabun da soke dokar.

Karin bayani