Asusun ajiyar rarar mai ya rame —Sanusi

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Malam Sanusi Lamido Sanusi

Gwamnan babban bankin Nigeria- CBN, Malam Sanusi Lamido Sanusi, ya ce kudin dake cikin assusun ajiyar rarar man fetur na kasar ya koma dala $2.5 biliyan daga $11.5 biliyan a cikin shekara guda.

Gwamnan wanda ya tabbarwa da BBC hakan, ya kara da cewar kudaden ajiyar kasar a kasashen waje ya koma $43.26 biliyan daga $45.26 a cikin watanni goma sha biyun da su ka wuce.

A cewar, Malam Sanusi, hakan na shafar yadda ake musayar kudi daga naira zuwa dalar Amurka.

Sai dai ya ce ba za a rage darajar kudin kasar ba wato naira, duk da irin wannan gibin da aka samu.

Masana harkokin tattalin arziki sun yi gargadin cewar kasar za ta iya fuskantar faduwar darajar kudinta da kuma hauhawar farashin kayayyaki sakamakon zabukan dake tafe a kasar a shekara ta 2015.

Karin bayani