Ana sa ran tsagaita wuta a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An shiga rana ta biyu na tattaunawa kan rikicin Syria

Jakadan kasashen duniya na musamman a Syria Lakhdar Brahimi zai gana da wakilan bangarorin biyu da suke halartar taron sasanta rikicin Syria a Switzerland.

Ganawar da aka yi a ranar farko ta bayyana wawakeken gibin da ke tsakanin gwamnatin shugaba Bashar al-Assad da kungiyoyin 'yan adawa.

Mr Brahimi ya amince da cewa har yanzu bai sani ba ko bangarorin biyu za su amince su zauna a daki guda dan tattaunawar.

Manufar ganawar da zai yi da su ranar Alhamis ita ce don ya auna shin za su iya aiki da juna sannan kuma wadanne batutuwa ne za a tattauna a kansu idan an fara ganawar gadan-gadan a ranar Juma'a.

Karin bayani