APC za ta dakile bukatun PDP a majalisa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gwamnan Rivers Rotimi Amaechi na fuskantar matsi daga gwamnatin tarayya.

Jami'yyar adawa ta APC a Nigeria ta umarci 'yan majalisunta na tarayya da su taka wa kasafin kudin 2014 birki da kuma kin tabbatar da wadanda aka bada sunayensu a makaman soji da na siyasa har sai an dawo da bin doka da oda a Jihar Rivers.

Jam'iyyar dai ta zargi jami'an tsaro a Rivers da yi wa jam'iyyar PDP aiki gami da hada baki da su inda suka zayyano jerin musgunawa da kuma cin zarafi da jami'an tsaro su ka yi wa gwamnan jihar Rotimi Ameachi.

Sai dai PDP ta ce umarnin da APC ta bayar kokarin hargitsa kasa ne kawai.

Wannan matsayar ta biyo bayan wani taro ne da kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC din ya gudanar a daren Juma'a.

Karin bayani