Ba zan amsa gayyatar SSS ba —El-Rufa'i

Elrufai ya ce babu wata doka da ta bai wa jami'an SSS damar kama mutum ba tare da sammacin kotu ba
Bayanan hoto,

Elrufai ya ce babu wata doka da ta bai wa jami'an SSS damar kama mutum ba tare da sammacin kotu ba

Mataimakin Sakataren riko na jam'iyyar APC a Nigeria, Nasir El-Rufa'i, ya ce ba zai amsa gayyatar da hukumar tsaro ta farin kaya, wato SSS, ta yi masa ba.

Hukumar ta SSS ta gayyace shi ne ya amsa tambayoyi saboda kalaman da ya yi cewa za a samu tashe-tashen hankula idan hukumar zaben ba ta gudanar da sahihin zabe a shekarar 2015 ba.

El-Rufa'i ya shaida wa BBC cewa dokar kasar ta hana jami'an tsaro kama mutum muddin ba ta karbi sammaci daga kotu kan hakan ba.

Ya kara da cewa ya kai hukumar SSS kara don haka ba zai amsa duk wata gayyata da za ta yi masa ba, yana mai cewa hakan ka iya yin barazana ga rayuwarsa.

Tsohon ministan na Abuja ya ce zai dauki dukkan matakan da suka dace na shari'a don ganin an hukunta hukumar ta SSS.