Hong Kong za ta kona hauren giwa

Hakkin mallakar hoto ivory
Image caption Hong Kong ce mashigar hauren giwa zuwa China.

Mahukuntan Hong Kong sun ce su na shirin lalata kimanin ton 30 na hauren giwa bayan da China, Amurka da Philippines su ka yi haka.

Jami'ai sun ce za a kone kaso 99% na hauren giwar da aka kama a yankin cikin shekaru masu zuwa, abin da ya rage kuma za a yi amfani da shi wurin gudanar da binciken kimiyya da kuma ilmantarwa.

Hong Kong ita ce mashigar haramtattun hauren giwa zuwa China, kuma masu fafutuka sun sha kiran ta dauki wannan mataki domin nuna da gaske take a kokarin dakile cinikin.

Masu fafutuka dai na ganin fataucin hauren giwar a China na kara yawan farautar giwa ba bisa ka'ida ba a Afrika.

Karin bayani