Nijar- Ana ci gaba da tsare Kakakin Jam'iyar CDS Rahama

Gidan Yari a Niamey babban birnin kasar Nijar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gidan Yari a Niamey babban birnin kasar Nijar

A Jamhuriyar Nijar hukumar 'yan sanda ta PJ na ci gaba da tsare kakakin Jam'iyar adawa ta CDS Rahama,da kuma editan jaridar l'Enqueteur.

A ranar Juma'a ne hukumar 'yansandan ta PJ mai kula da bincike kan manya-manyan laifuka ta cafke kakakin na jam'iyar adawar kasar ta CDS Rahama Alhaji Dudu Rahama.

Sai dai ya zuwa yanzu hukumar yan sandan ba tayi wani bayani ba a game da dalilan da suka sa ta tsare wadannan mutanen.

Amma wasu rahotanni na cewa hakan ba zai rasa nasaba da wasu matakai da gwamnatin kasar ta dauka a baya bayan nan na kama wasu mutane da tace sun furta wasu kalami marasa dadi a kafafen yada labarai.

Tsare editan jaridar l'Enqueteur Malam Sumana Idrisa Maiga na zuwa ne duk da gwamnatin a shekara ta 2012 ta yi na'am da wata dokar hana tsare duk wani dan jarida a gidan kaso, da wasu ke ganin an gaza aiki da ita.