Ribar Samsung ta ragu

Hakkin mallakar hoto samsung

Kamfanin samar da wayoyin salula da talabijn mafi girma a duniya, Samsung Electronics ya ba da rahoton raguwar ribarsa ta watanni uku, a karo na farko cikin shekaru biyu.

Tsabar ribar Naira tirilyan daya ya samu daga Oktoba zuwa Disamba, abinda ya gaza na watanni ukun baya da kaso 11%.

Ribar Samsung ta ragu ne sanadiyyar raguwar ribar da kamfanin ke samu a cinikin wayoyin salula.

Haka kuma wata salalar musamman da kamfanin ya biya da kuma faduwar darajar kudin kasar Koriya, wato Won sun kara samar da gibi a ribar kamfanin.

Samsung dai ya ba ma'aikatansa salalar N11.2 triliyan a cikin watanni ukun domin bikin cikar shekaru 20 da kaddamar da sabon tsarin tafiyar da kamfanin da shugabansa Lee Kun Hee ya kirkiro, abinda ake ganin shi ya haddasa bunkasarsa.

Bugu da kari sauye-sauyen da ake samu a darajar kudin Koriya ya sa ta yi asarar kimanin N10 triliyan.

Kamfanin ya ce zai wuya ya kara ribarsa ta karu a cikin watanni ukun farkon bana saboda akwai karancin cinikin talabijin a irin wannan lokaci.

Karuwar kasayya

Hakkin mallakar hoto AFP

A 'yan shekarun nan dai Samsung na kara bunkasa ne sanadiyyar karbuwar wayoyinsa na komai-da-ruwanka.

Wannan ne ya sa kamfanin maye gurbin Nokia a matsayin kamfanin samar da wayar tarho mafi girma a duniya a shekarar 2012.

Sai dai kamfanin na Koriya ta Kudu na fuskantar kasayya a kasuwar bayan da manyan abokan gogayyarsa su ka kaddamar da sababbin wayoyi.

Daya daga cikin manyan abokan kasayyar Samsung, Apple ya kaddamar da sababbin wayoyi biyu samfurin iPhone - 5S ta masu kudi da 5C ta talakawa - a watan Satumban bara.

Nokia - wanda Microsoft ya sayi bangaren samar da wayoyinsa - ya kaddamar da sababbin wayoyi biyu a Satumba, yayin da kamfanin HTC na Taiwan ya kaddamar da sabuwar waya a Oktoba.

Manazarta na ganin samur sababbin wayoyin ya taba cinikin Samsung tsakanin Oktoba da Disamba.

A sanarwar da Samsung ya fitar game da kudin shigarsa, ya ce ya na hasashen gasa za ta karu a bana kuma wasu kamfanonin za su rage farashi domin samun karbuwa a kasuwa.

Idan hakan ta faru, ribar da za a ci za ta kara raguwa.

Shekarar tarihi

Duk da raguwar ribar a watannin karshen shekara, Samsung ya samu ribar da bai taba samun kamarta ba a bara.

Tsagwaron ribar da kamfanin ya samu a 2013 ta kama N42.5 tiriliyan, abin da ya dara ribar 2012 da kaso 28%.

Kamfanin ya ce har yanzu shi ne kan gaba wurin samar da kwamfutocin tafi-da-gidanka da kaso 30% na kasuwar na'urorin a kasashen da su ka ci gaba da masu tasowa.

Samsung ya ce zai fitar da sababbin wayoyin komai-da-ruwanka da kwamfutocin hannu, tare kuma da shiga harkar na'urorin fasaha da ake iya sa wa a jiki domin habaka ribarsa.