Rikici ya kara ta'azzara a Ukraine

Zanga-zanga a kasar Ukraine Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zanga-zanga a kasar Ukraine

Rikici na karuwa a Kiev, babban birnin kasar Ukraine sa'oi kadan bayan da shugaba Viktor Yanukovych ya yi alkawarin yin garanbawul ga gwamnatinsa.

Wani wakilin BBC dake birnin Kiev ya ce ya ga wuta na ci ganga-ganga a tsakiyar birnin bayan da masu zanga-zanga suka kona tayoyi.

Masu zanga-zangar sun yi ta jifan 'yansanda da duwatsu, bama-bamai da suka hada da wuta, inda su kuma suka rika mayar da martani da hayaki mai sa hawaye da harsasan roba.

A baya dai daya daga cikin shugabannin 'yan adawa Vitaly Klitschko ya sake kira ga shugaban kasar ya yi murabus, a matsayin wata hanya kadai da za ta kawo karshen zanga-zangar da ta bazu a fadin kasar.

Masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin sun kara fadada shingaye a Kiev babban birnin kasar, suka kuma kwace ikon ma'aikatar gona.

Sun kuma mamaye ofisoshin gwamnati a biranen kasar da dama.

Cikin fushi dai sun yi ta ife-ife suna cewa dan fashi, dan fashi a wajen ofisoshin kananan hukumomi a Chernivtsi dake kudu maso yammacin kasar

Shi dai shugaba Yanukovitch ya yi gargadin daukar matakai masu tsauri muddin tashin hankalin da ya babaibaye kasar ya kara ta'azzara.