An kashe masu zanga zanga a Masar

Zanga-zanga a Masar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zanga-Zanga a Masar

Jami'an tsaro a Masar sun ce an kashe masu zanga zanga akalla 29 lokacin arangama a Alkahira, da sauran biranen kasar, a lokacin gangamin da magoya bangarori biyu masu adawa da juna ke yi.

'Yan sanda a Masar sun yi amfani da borkonon tsohuwa a kan masu zanga-zagar nuna kin jinin gwamnati a Al-kahira, babban birnin ta.

An kuma tsaurara matakan tsaro don bukukuwan da ake yi na cika shekaru ukku da boren da ya kifar da gwamnatin Hosni Mubarak.

Masu zangar sun hada da 'Yan uwa Musulmi da kuma magoya bayan gwamnati mai ci.

Zaman dar dar ya karu bayan da wasu bama bamai suka fashe a Al-kahira a jiya Juma'a.

A yau ma wani bam din ya fashe.

Karin bayani