Hollande ya rabu da abokiyar zaman sa Valerie

Shugaban Faransa Hollande Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Faransa Hollande

Shugaban Faransa Francois Hollande ya ce zasu rabu da abokiyar zamansa da suka jima tare wato Valerie Trierweiler.

Matakin dai ya biyo bayan zarge-zargen cewa yana lalata da wata 'yar fim mai suna Julie Gayet.

Dama ana ta maganganu a kan makomar zaman nasu tun bayan da wata mujalla ta yi zargin cewa yana cin amanar abokiyar zaman tasa.

Ya ce zai yi karin haske a kan maganar kafun wata ziyara da ya shirya kaiwa Amurka.