An yi wa 'yan adawa tayin mukami a Ukraine

rikici a Ukraine Hakkin mallakar hoto AP
Image caption rikici a Ukraine

Shugaban Ukrain Viktor Yanukouchh yayi wa shugabannin adawan kasar tayin mukamai a gwamnatin sa.... a wani yunkurin kawo karshen tashin hankalin da kasar ke fama da shi.

Shugaban ya ce zai baiwa Arseniy Yatsenuyk mukamin Praminista kuma ba matsala idan Vitaly Klitschko ya zama mataimakin Praminister.

Ya fidda sanarwar ce a shafin sa na internet bayan wata tattaunawa da 'yan adawa a kan yadda za a warware rikicin kasar.

Masu zanga zanga sun ce mafita ita ce kawai shugaba Yanukouchh kasar ya sauka