Najeriya- Kisan dan kasar China a jihar Filato

Taswirar Jihar Filato a Najeriya
Image caption Taswirar Jihar Filato a Najeriya

Hukumomin tsaro a jihar Filaton Nijeriya sun yi karin haske kan wani hari da aka kai kan wasu ma'aikata 'yan kasar China a yankin Riyom na jihar.

A ranar Juma'a da ta gabata ne dai aka kai harin a kauyen Atakar dake karamar hukumar Riyom mai makotaka da jihar Kaduna.

Kwamishinan 'yan-sandan jihar ta Filato Mista Chris Olakpe ya tabbatarwa da BBC kashe dan kasar China da kuma jikkata dan sanda guda dake masu rakiya, amma yace kawo yanzu ba a kama wani da ake zargi da aikata kisan ba.

Bayananai sun sha bamban kan hakikannin abin da yan kasar Chinar ke yi a yankin, inda wasu bayanai ke cewa dama suna gudanar da wani aikin kwangilar da ta shafi samar da wutar lanatarki, wasu bayanai kuma na cewa suna aikin layin dogo ne.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga ofishin jakadancin China a Nijeriya game da harin da aka kai way an kasar a jihar Filaton Nijeriya.