Amurka ta soki sakin fursunonin Afghanistan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana zargin wasu fursonin da kashe sojin Afghanistan

Rundunar sojin Amurka a Afghanistan ta yi tur da shirin da ake yi na sakin wasu fursunoni da ta ce na barazana ga tsaro.

Amurkawan sun ce wannan ci baya ne ga yunkurin tabbatar da ikon doka a Afghanistan.

Ana sa ran gwamnatin Afghanistan za ta fara sakin mutane 37 daga cikin fursunoni 88 da za a sallama duk da Amurka ba ta amince da sakinsu ba.

Amurka ta ce da yawansu na da alaka da kai hare-hare kan jami'an tsaron Afghanistan.