"Babu matsalar leken asiri a Nigeria"

Image caption Ofishin Hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, a Nigeria.

Rundunar sojin Nigeria ta musanta cewa ta na samun matsalar tattara bayanan leken asiri daga hukumar tsaro ta SSS a yakin da take yi da masu tada kayar baya a kasar.

An dai kwashe lokaci mai tsawo ana arangama da 'yan kugiyar Jama'atu Ahlisunnah lidda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko-Haram da kuma jami'an tsaro a arewacin kasar .

Mahukunta sun dauki matakai daban-daban da nufin murkushe 'yan kungiyar, amma har yanzu matsalar ba ta kau ba, musamman ma a shiyyar arewa-maso-gabashin kasar.

To, sai dai yayinda wasu ke ganin gazawar jami'an tsaro na leken asirin miyagu shi ke kawo cikas wajen kawo karshen hare-haren, a na su bangaren jami'an tsaron na ganin al'umma na da rawar da za ta taka wajen inganta tsaron ta hanyar bayar da bayanai.

Wannan rahoton na zuwa ne a jerin rahotannin musamman kan batutuwan da su ka shafi leken asiri a kasashe daban-dabam da sashen Afrika na BBC ke gabatarwa a wannan Litinin din.

Karin bayani